‘Yan bindiga sun kai hari jami’ar jihar Plateau.
Hukumomin jami’ar jihar Plateau (PLASU) da ke tsakiyar Najeriya sun ce jami’an tsaron makarantar sun daƙile wani harin ‘yan bindiga da suka kai makarantar ranar Talata da daddare.
‘Yan bindigar sun mamaye ɗakunan kwanan ɗalibai mata a makarantar da ke Bokkos a cikin dare, kamar yadda hukumomin makarantar suka bayyana, to sai dai sun ce ‘yan bindigar ba su kama ɗalibai ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar John Agams ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN faruwar lamarin.
Mista Agams ya ce ‘yan bindigar sun je jami’ar ne da nufin yin garkuwa da ɗalibai, to amma jami’an tsaron makarantar sun samu nasarar daƙile harin.
”Da gaske ne ‘yan bindiga sun yi yunƙurin sace wasu daga cikin ɗalibanmu, to amma jami’an tsaron makarantar sun daƙile yunkurinsu”, in ji Mista Agams.
Ya ƙara da cewa ɗaliba ɗaya ta samu rauni sakamakon lamarin da ya faru.
Shugaban jami’ar Farfesa Benard Matur ya yi kira ga ɗaliban da su kwantar da hankali.
Read More ;
Financial Times: Saudiyya ta tashi daga warware matsaloli zuwa diflomasiyya.
lokaci bayan lokaci tare da gwagwarmayar Falasdinawa; Harin roka ya kai Tel Aviv.
Kubucewar sahyoniyawan daga matsugunan da ke makwabtaka da Zirin Gaza a rana ta biyu a jere.