Yan bindiga sun hallaka mutane biyu a gidan mai na jihar Anambra.
Yan bindiga sun kai hari gidan mai na P&F dake Nnokwa a garin Idimile kudancin jihar Anambra, inda sukayi sanadiyyar rayukan mutane biyu.
Lamarin ya faru ne a ranar sati a gidan man dake kusa da coci Mary Catholic a garin Nnokwa.
Mutanen dake wurin sun tabbatar da cewa yan bindigan sun kashe manajan gidan manne mai suna Marvelous tate da abokinsa mai suna Richards yayin da suka je sayo abinci.
READ MORE : Putin; Duk Kasar Da Ta Hana Shawagin Jirage, Ta Shiga Yakin Ukraine