Akalla mutane 32 suka mutu sakamakon hare hare daban daban daga kungiyoyi ‘yan bindiga a sassa daban daban na Najeriya a makon da ya gabata.
Akasin yadda lamarin yake a makonnin da suka wuce, inda akasarin kashe kashen sun auku a arewa masdo yammacin kasar, inda ‘yan bindiga ke cin zalin wadanda ba su jib a ba su gani ba, an fi samun kashe kashen a yankin arewa ta tsakiyar kasar.
A wani labarin na daban Dan wasan gaba na PSG da Faransa Kylian Mbappe ya ci wa Paris Saint-Germain kwallo 100 a gasar Ligue 1, a wasan gasar na Faransa da suka doke Monaco da ci 2-0 a filin Parc des Princes ranar Lahadi.
Dan wasan na Faransa, wanda yanzu ne ya cika shekaru 23 a farkon wannan wata, ya ci wa Monaco kwallaye 16 a gasar lig a farkon kafin rabuwa da kungiyar.
Nasarar ta bai wa PSG damar kara tazarar maki 13 a teburin Ligue 1 da maki 13 gaban Marseille, wadda itama ta samu nasara a kan Strasbourg da ci 2-0 a ranar Lahadin da ta wuce kuma tana da wasa a hannunta.