‘Yan bindigar da suka sace Sarkin Kajuru dake Jihar Kaduna Alhaji Alhassan Adamu tare da jama’ar sa sun bukaci a biya su diyyar naira miliyan 200 kafin su sake shi da mutanen dake cikin tawagar sa.
Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a kasar ta jiyo daya daga cikin masu nadin Sarkin Kajuru na tabbatar cewar Yan bindigar sun tintibe su domin gabatar da bukatar su ta karbar diyyar.
Basaraken yace suna ci gaba da tattaunawa da su da zummar ganin an kubutar da Sarkin da kuma jama’ar sa daga hannun mutanen da suka yi garkuwa da su.
Rahotanni sun ce Sarki Adamu ya shaidawa jami’an tsaro barazanar da suke fuskanta sa’oi 48 kafin Yan bindigar su kai musu hari.
Allon makarantar Bethel Baptist da ‘yan bindiga suka sacewa dalibai 121 a karamar hukumar Chikun dake jihar Kaduna.
‘Yan’uwan Sarkin da wasu daga cikin Yan majalisar sa sun shaidawa Jaridar cewar Basaraken mai shekaru 85 ya gana da jami’an tsaro a ranar juma’ar da ta gabata, inda ya shaida musu barazanar dake yake fuskanta, yayin da wani jami’in gwamnati yace kwamandan sojin dake yankin ya baiwa Sarkin shawara dangane zirga zirgar da yake da kuma bukatar kara sanya ido.
Jami’in ya ce wannan ya biyo bayan labarin da suka samu daga wani da akayi garkuwa da shi ya kuma kubuta cewar Yan bindigar sun bukaci lambar wayar Sarkin.
Bayan ya shaida musu cewar bashi da lambar, Yan bindigar daga bisani sun ce masa sun same ta, kuma zasu kai masa hari, abinda ya sa mutumin ya shaidawa Sarkin halin da ake ciki.
Jihar Kaduna na daya daga cikin jihohin da hare haren Yan bindiga da garkuwa da mutane domin karbar diyya ya zama ruwan dare tare.
Gwamnatin Jihar bata tattaunawa da Yan bindiga ballanata biyan diyya domin kubutar da wadanda akayi garkuwa da su.
Yanzu haka daliban makarantu da kuma mutanen gari da dama na hannun Yan bindigar suna garkuwa da su.