‘Yan Arewa ma zasu iya tsayawa takara a 2023 _Inji PDP ..
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa babu maganar karba-karba a tsarinta.
Hakan na zuwa ne yayin da ‘yan kudu da yawa ke ihun sai an barsu sun tsaya takara saboda a yanzu lokacinsu ne.
Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da sauran wasu ‘yan Arewa ne ke neman tsayawa takarar shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
Saidai suna shan suka daga kudu cewa, ya kamata su bari ‘yan kudu kadai su nemi takarar.