‘Yan adawa a kasar Mali, sun sanar da cewa zasu yanke kauna ga hukumomin rikon kwarya na kasar daga ranar 25 ga watan Maris mai zuwa.
kawancen jam’iyyun da ya hada da jiga-jigan jam’iyyu na kasar sun kuma bada wasu shawarwari na fitar da kasar daga cikin halin da take ciki.
Bangarorin sun kuma bukaci a kafa wata sabuwar gwamnatin wucin gadi wacce wani firaminista marar bangaranci zai jagoranta.