‘Yan adawa sun nuna ɓacin ransu kan yunƙurin wa’adi na uku a CAR
Daruruwan masu zanga-zanga ne suka fantsama kan titunan Bangui babban birnin Jamhuriyar Airka ta Tsakiya a ranar Juma’a domin nuna adawa da shirin gwamnatin ƙasar na yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima, domin bai wa shugaban ƙasar Faustin-Archange Touadera damar sake tsayawa takara a wa’adin mulki na uku.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa, shugabanin adawar ƙasar ne suka jagoranci masu zanga-zangar su aƙalla 500 a birin na Bangui, tare da rakiyar jami’an tsaron kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
Tun da farko gwamnatin ƙasar ta haramta zanga-zangar, to amma shugabanin adawar suka buƙaci jami’an kiyayen zaman lfiyar na MDD su ba su kariya a lokacin gudanar da ita.
A ranar 30 ga watan Yuli ne za a kaɗa ƙuri’ar amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar gyara.
A watan Mayun da ya gabata ne, shugaba Touadéra ya bayyana cewa za a yi wa kundin tsarin mulkin kasar garambawul.
Idan har matakin ya yi nasara to za a cire batun taƙaita wa’adin mulki a kundin tsarin mulkin ƙasar, lamarin da zai bai wa shugabana ƙasar damar sake tsayawa takara a wa’adin mulki na uku, kamar yadda magoya bayansa ke fata.
A shekarar 2020 ne shugabar kotun tsarin mulkin Farfesa Danièle Darlan ta ce shirin yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, ya saɓa wa doka, musamman batun ƙara wa’adin mulkin shugaban kasa.
Kalaman da suka sanya aka sauke ta daga muƙamin tare da maye gurbinta da Jean-Pierre Waboé, wanda ake ganin makusanci ne ga shugaban kasar.
Tsohon firaministan ƙasar, kuma ɗan majalisar jam’iyyar adawa Martin Ziguele ya ce, ”Touadera na son zama mai mulkin kama-karya, shi ya sa muke adawa da gyaran dokar, wadda ba komai ba ce, face zambar siyasa”
A shekarar 2016 ne aka fara zaɓen Touadera a matsayin shugaban ƙasa da taimakon Faransa da Majalisar Dinkin Duniya, haka kuma an sake zaɓensa a 2020 a zaɓen da ya sha suka kan rashin fitowar masu kaɗa ƙuri’a, musamman a yankunan da ‘yan tawate ke riƙe da su.