Yakin basasar Sudan rikici ne na soji tsakanin bangarorin da ke adawa da gwamnatin mulkin sojan Sudan. Wannan rikici ya fara ne a ranar 15 ga Afrilu, 2023 tare da afkuwar fadan soji a duk fadin kasar, musamman a Khartoum da Darfur. Ya zuwa ranar 21 ga Afrilu, akalla mutane 413 ne suka mutu sannan fiye da mutane 3,500 suka jikkata. Rikicin dai ya faro ne a lokacin da ‘yan ta’addar Rapid Response Force (RSF) suka kai hari a muhimman yankunan gwamnatin kasar. Bangarorin da ke rikici da juna duk sun yi ikirarin iko da muhimman yankunan gwamnati.
Ci gaba da rikice-rikice sun kara haɗarin ƙarin tarwatsewa. A baya dai an tabo batun raba Sudan zuwa kasashe takwas. Ci gaba da yakin na iya haifar da raba kasar Sudan zuwa kasashe uku:
- 1) Kordofan a cikin cibiyar da yanki na 376 dubu murabba’in kilomita
- 2) Darfur a yamma mai fadin murabba’in kilomita dubu 493
- 3) Sudan a arewa mai fadin kimamin murabba’in kilomita dubu 900
Babban sakatare janar na MDD, Antonio Guterres, ya yi, tir da abunda ya danganta da juyin mulkin soji dake faruwa a Sudan, tare da kiran a gaggauta sakin dukkan manyan ‘yan siyasa da ake tsare da ba tare da wata wata ba.
Kungiyar tarayyar Afrika ma ta fitar da irin wanan sanarwa inda ta bukaci sojoji da farar hula a kasar dasu koma tattaunawa a tsakaninsu domin ceto kasar daga halin da ta tsunduma.
Kungiyar kasashen Larabawa ita ma ta bukaci dukkan bangarorin dasu mutunta yarjejeniyar raba mulkin rikon kwarya da suka cimma a 2019, bayan kifar da mulkin Umar Al-bashir.
Duba nan: Zuciyar Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Ta Karye Dangane Da Gaza Da Sudan
Kwamitin kungiyar tarayyar turai kuwa ya bukaci da kaucewa zubar da jinni.
Shugaban faransa Emanuel Macron, ya bukaci a mutunta hurimin firaministan na Sudan da kuma na magabata ‘yan siyasa.
- Amurka dai ta ce ta dakatar da tallafin jin kai da take baiwa kasar ta Sudan.
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran kwamitin tsaron MDD, zai yi zama kan hali da ake ciki a kasar ta Sudan, bayan da juyin mulkin da sojoji sukayi tare da kame mambobin gwamnatin rikon kwarya ciki har da firaminista Abdallah Hamdok.
Duba nan: Dalilai 3 da bai kamata a manta da kutsen da Rasha ke yi wa Najeriya ba
Duba nan: An kama kimanin mutun 1,000 a zanga-zangar #EndBadGovernance a Kano