Shafin yada labarai na Palestine yaum ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin yahudawan sahyuniya ta sake kame 4 daga cikin Falastinawa 6 da suka tsere daga gidan kaso a cikin wannan mako.
Bayanin ya ce tun bayan da Falastinawan suka tsere daga gidan kason, jami’an tsaron gwamnatin yahudawan suke ta farautarsu, inda suka kama dangin wasu daga cikin Falastinawa suka tsare su.
Amma ya zuwa yanzu dai jami’an tsaron yahudawan sun iya kama hudu daga cikin Falastinawan, kuma sun sake mayar da su a gidan kaso.
A nasu bangaren kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa sun gargadi Isra’ila kan daukar duk wani mataki na taba lafiyar Falastinawan, domin taba su yana a matsayin taba dukkanin al’ummar Falastinu ne.
Yanzu haka dai akwai dubban Falastinawa da suke tsarea cikin gidajen kason yahudawan Isra’ila, mafi yawa daga cikinsu Isra’ila na zarginsu da kasancewa mambobin kungiyoyin gwagwarmaya da da mamayar ad take yi wa kasarsu ne.
A wani labarin nadaba bangaren yada labarai na hubbaren Imam Hussain (AS) ya sanar da cewa, an fara shirin tarbar baki masu shirin gudanar da ziyarar arba’in na Imam Hussain (AS) a wannan shekara.
Shugaban kwamitin kula da shirya taruka a hubbaren Imam Hussain (AS) Sayyid Sadeq Samir Alyasiri ya bayyana cewa, an fara shirin tarbar masu ziyara kamar yadda aka saba yi a kowace shekara.
Ya ce kamar shekarar bara, a shekarar bana ma dukkanin shirye-shiryen suna kasancewa ne bisa tsauraran matakai na kiwon lafiya, sakamakon yaduwar cutar corona.
Baya ga haka kuma ya bayyana cewa, an yi tsare-tsare a bangaren yadda tarukan za su kasance da kuma da kuma wuraren hutuwa ga matafiya da suke shigowa Karbala daga bangarori daban-daban na birnin.
Ya ci gaba da cewa, dangane da matakan tsaro kuwa, tun daga lokacin tarukan Ashura da aka gudanar sama da wata guda da ya gabata, har yanzu dubban jami’an tsaro suna cikin shiri a dukkanin sassa na birnin da kuma hanyoyin da ke isa birnin daga birane daban-daban na kasar Iraki.