Yadda zaman kotun kalubalantar nasarar Bola Tinubu ya kasance a Abuja.
An shiga rana ta biyu na ci gaba a sauraron kararrakin da suka shafi zaɓen shugaban kasa da aka yi a Najeriya.
Kotun sauraron kararrakin wadda ke zamanta a Abuja, babban birnin kasar, ta saurari lauyoyi daga ɓangaren jam’iyyar adawa ta PDP da ɗan takararta da kuma jam’iyyar adawa ta APM.
Jam’iyyun dai na kalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC mai muki ya samu a zaɓen.
Kotun sauraron karrarakin zaɓen wadda ta zauna karkashin alkalai biyar da mai shari’a Haruna Tsammani ke jagoranta ta fara ne da sauraron karar jam’iyyar adawa ta APM ta shigar a zaman share fagen sauraron karrarakin da ta yi a yau Talata.
Jam’iyyar ta APM ta shaida wa kotun cewa ta bayar da dukkannin bayanan da ake bukata da kuma amsoshin a takardar bayanan share-fagen sauraron karrarakin na “FORM TF 008”.
Yayin da lauyoyin wadanda ta ke kara, wato hukumar zaɓe ta kasa INEC da jam’iyyar APC mai Mulki da dan takararta da mataimakinsa, Kashim Shettima da Ibrahim Kabiru Masari su ma sun bayyana cewa sun mayar da martani kan tambayoyin da suka shafi karar.
Sai dai lauyan Bola Ahmed Tinubu ya shaidawa kotun cewa ya shigar da wata bukata wadda ke neman a yi watsi da karar da jam’iyyar ta APM ta shigar, saboda rashin makama.
Inda su ma lauyoyin wanda ake karar suka bukaci kotun ta yi watsi da karar.
Ita dai jam’iyyar ta APM tana kalubalantar nasarar da Bola Tinubu ya samu saboda magudin zaɓe da tashe-tashen hankulan da aka samu a lokacin zaɓen.
Amma mai shari’a, Tsammani ya umarci dukkanin ɓangarorin da su je su haɗe batutuwan da bukatunsu guri guda domin sauraronsu a zama na gaba.
A yau Talata din ne kuma kotun ta saurari karar da jam’iyyar PDP da ɗan takararta, Alhaji Atiku Abubakar suka shigar, bayan ta dawo daga ɗan gajeren hutun da ta yi.
PDP da Atiku na neman kotun ta ayyana Alhaji Atikun a matsayin wanda ya lashe zaben ko a je zabe zagaye na biyu tsakaninsa da Bola Tinubu ko kuma a soke baki ɗaya zaɓen a sake sabo.
Sun yi ikirarin cewa Tinubu bai samu halattaun kuru’u masu rinjaye ba, sannan bai cancanci tsayawa Takara ba a lokacin da aka yi zaɓen.
Sai dai lauyan shugaban mai jiran gado ya shigar da bukatar korar karar, mai shari’a Tsammani ya ce sai a zama na gaba kotun za ta duba wannan bukatar.
Haka kuma za ta duba bukatar da lauyoyin tsohon mataimakin shugaban kasar ya shigar tun da fari na neman a watsa zaman kotun kai-tsaye .
Duka kararrakin biyu dai kotun ta ɗagesu zuwa ranar Alhamis mai zuwa, wato 11 ga watan Mayun da muke ciki.
A ci gaba da zaman sharar-fagen da take yi.