A ci gaba da kokarin ganin yadda za’a hada kai tare da fahimtar juna a tsakanin mabiya manyan addinan Najeriya guda biyu, Cibiyar Daidaita Mabiya Addinai ta hada kan limamai da Pastoci.
Wannan yunkuri ne domin su fitar da kundin dokoki da zai taimaka wajen yin wa’azi a kasar, sai dai wasu na ganin ba a nan gizo ke saka ba.
Cibiyar Daidaita Mabiya Addinan ta dauki wannan matakin ne domin kaucewa furta kalamai da za su iya harzuka jama’a ko cin zarafin wasu da sunan addini a kasar.
Daya Daga cikin wadanda suka halarci taron shi ne limamin Masallacin Wharff Road a Kaduna, Mohammed Sani Isah.
Imam Sani ya ce, wake daya ke bata gari domin wasu ne masu wa’azin addinin Musulunci da wasu masu wa’azin addinin Kirista, su ne ba su tsare ka’idojin da addinin kamar yadda ya bada ba.
Ya ce da kowa zai tsare ka’idojin addinan da babu dalilin rubuta wani kundi, saboda yadda Qur’ani da hadisan Manzon Allah SAW sun ishi ko wane Musulmi su koya ma shi yadda ya kamata ya yi wa’azi ko magana.
Hakazalika, litattafan da Kiristoci suka ba da gaskiya da su, sun ishi kowane Kirista ya yi koyi da su.
Sani ya kara da cewa wasu suna bata masu aikin, shi ne suka ce to bari su yi wa kansu wasu sharruda da za su tunatar da su abubuwan da suka dace da addinan biyu.
Shi ma Rev. James Movel Wuye yana cikin masu halartar taron. Ya yi tsokaci akan hujjojin yin kudinin, ya ba da misali da yadda wasu masu wa’azi ke amfani da dandalin sada zumunta wajen yada labaran karya, da kazafi, da cin mutuncin addinan juna.
Wuye ya ce dole ne a yi wa tukka hanci domin idan an bari wannan abu ya ci gaba zai sa a ci gaba da yin gasa na wanene ya fi kisa a tsakanin mabiya addinan. Sannan ya kara da cewa wannan mataki ne mai kyau.
Sai dai daya cikin jigajigan kungiyar Amir Mohammed Jamil ya yi kira ne ga matasa ‘yan uwansa da su nemi abin dogaro da kai saboda a daina amfani da su wajen haifar da tashin hankali saboda wani kudi kalilan da za a ba su.
Abin jira a gani shi ne irin tasirin ɗa kundin zai yi wajen rage banbancen da ke baiyana a tsakanin addinan musamman ma ta hanyar wa’azi.