Sadiq Ango Abdullahi, ‘dan shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, ya shaki iskar ‘yanci a ranar Sallah Hotunan shi na baya da na yanzu, zasu tabbatar da cewa fasinjojin da aka sace suna shan matukar wahala a wurin ‘yan ta’addan.
A hotunan matashin ‘dan siyasan na baya, ya kasance ‘dan kwalisa da iya ado, amma bayan sako shi ya koma kamar a zubda masa da hawaye.
Sadiq, ‘dan shugaban kungiyar dattawan arewa, Farfesa Ango Abdullahi, wanda aka yi garkuwa da shi a farmakin jirgin kasan da ‘yan ta’adda suka kai ranar 28 ga watan Maris, ya canza kamanni kwata-kwata daga yadda yake a baya kafin yayi watanni uku a daji.
Sadiq yana daga cikin mutum bakwai da ‘yan ta’addan suka sako a ranar Asabar, 9 ga watan Yulin 2022.
Idan za a tuna, a wani bidiyo da aka saki a watan Mayu, Sadiq wanda yayi nasarar lashe zaben fidda gwani na majalisar wakilai a Zaria, jihar Kaduna duk da yana hannun ‘yan ta’adda, ya roki gwamnatin tarayya da ta kawo musu taimako inda yace da yawa daga cikin fasinjojin da aka sace basu da lafiya.
A kowacce rana, lamarin kara tabarbarewa yake yi. Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo mana dauki kafin mu fara rasa rayukansu,” yace. Ga hotunan shi na baya, da na lokacin da ‘yan ta’addan suka sako shi.
A yayin da Legit.ng ta so jin ta bakin wani makusancin Farfesa Ango Abdullahi, yace zai kira daga baya.