Yadda Amotekun ta kama mutum 151 daga arewacin Najeriya cunkushe cikin tirela biyu.
Ƙungiyar tabbatar da tsaro ta Amotekun da ke a kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta ƙara kama wasu matasa da yawansu ya kai 151.
Kungiyar ta ce matasan sun fito ne daga arewacin Najeriya.
Ana zargin su da cewa ‘yan ta’adda ne da ke neman yin kutse da kuma samun mafaka a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya.
To sai dai mutanen na cewa su ‘yan ci-rani ne da kan shiga kudancin kasar domin neman na halaliya.
Mutanen 151, kamar yadda kwamandan rundunar ta Amotekun Adetunji Adeleye ya nuna sun fito ne daga jihohin Katsina da Kano da kuma Jigawa.
Ya ce an kama su da layu da hotuna da ke nuna alamar samun horo na musamman.
Waɗanda ake zargin sun haɗa da wasu mata biyar da suka ɓoye a bayan buhunan wake da shinkafa a cikin tireloli biyu da aka gano a lokacin da jami’an Amotekun suka tsananta bincike.
Adetunji Adeleye ya bayyana cewa an kama manyan motocin da suka yi jigilar mutanen ne biyo bayan rahoton sirri da suka samu.
Ya ce, an tare motocin ne a kusa da hanyar Sango da Akure zuwa Ado, bayan da jami’an kungiyar sintirin suka fara zargin abubuwan da suke dauke da su cikin manyan motocin inda suka gano mutane cunkushe a ciki.
Ya ce, “mun kama wasu manyan motoci guda biyu dauke da mutane 151 da suka yi dubara suka boye a bayan buhunan shinkafa da wake, ta yadda ba za a iya sanin adadin mutanen da ke a cikin motocin ba.
“Bayan an kama su, mun yi masu tambayoyi, wasu sun ce za su je Akure a jihar Ondon, yayin da wasu suka ce Osogbo a jihar Osun.
Ko da yake, ba mu kammala daukan bayanansu ba, domin babu wani daga cikinsu da ya san abin da zai je yi ko kuma aikin da zai yi.
Abin da suka iya gaya mana shi ne, sun shiga motar ce suka zo Jihar Ondo,”in ji Mista Adeleye.
Shugaban na Amotekun ya ce a yayin da suke bincike ne suka gano ababen hawa, da suka hada da kekuna 10 da kuma layu iri-iri.
Sai dai ya ce idan suka bincika ba su sami komai a kansu ba, muddin ba su da wani wanda zai kula da su a jihar Ondo, za su tasa keyarsu domn mayar da su jihohinsu.