‘Ya kamata masu wawushe dukiyar gwamnati su zuba jari a cikin gida’
Babbar mai binciken kuɗi ta Kenya Nancy Gathungu ta buƙaci masu satar kuɗin gwamnati da su rinƙa amfani da kuɗin wajen zuba jari a cikin ƙasar.
Ta ce idan ana barin mutane suna zuba jari a cikin gida da kuɗaɗen da suka samu ta hanyar haram, hakan zai kawo ci gaba a ƙasa.
Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa kuɗi kimanin dala biliyan 2.6 ne manyan jagororin ƙasar suka jibge a bankuna da dama na ƙasashen ƙetare, waɗanda suka samu ta hanyar satar kuɗin gwamnati.
Ms Gathungu ta shaida wa masu halartar wani taro a Nairobi cewa “ya kamata mu fara yeƙuwar cewa idan har ka samu nasarar sace kuɗi ba tare da an kama ka ba, to ka zuba jari da ita a Kenya. Idan ka saci kuɗin al’ummar Kenya, ka zuba jari a Kenya.”
Ta ƙara da cewa “za a iya ganin abin kamar almara, amma akwai yiwuwar mu ga ana samun ci gaba a sanadiyyar haka, daga baya sai mu tuhume su, daga ina ku ka samo kuɗin?”
Ta ce wannan wata dubara ce da manyan masu bincike na ƙasashen yankin ke tunanin fara amafani da ita.
Ofishin babbar mai binciken ta Kenya ma’aikata ce mai zaman kanta, wadda kundin tsarin mulki ya ba ta ƙarfin lura da yadda ake kashe kuɗaɗen al’umma.