Ya kamata Buhari ya sauka daga mulki saboda ba zai iya magance matsalar tsaro ba – Ƙungiyar Dattawan Arewa.
Ƙungiyar Dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta nemi Shugban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki nan take sakamakon kashe-kashen da ake fama da su a faɗin ƙasar, musamman a arewaci.
Da yake magana cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, kakakin ƙungiyar Hakeem Baba-Ahmed ya ce Buhari “ba zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaro da ta addabe mu ba”.
“Da alama gwamnatin Buhari ba ta da abin cewa game da ƙalubalen tsaro da muke ciki. Ba zai yiwu mu ci gaba da zama ƙarƙashin ikon masu kisa ba, da masu garkuwa da mutane, da masu fyaɗe, da miyagun da suka hana mu ‘yancinmu na zama lafiya,” a cewar ƙungiyar.
Kiran nasu na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan ‘yan bindiga sun kashe kusan mutum 200 a Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, da kuma sace wasu ɗaliban kwaleji mata da aka yi a Jihar Zamfara ranar Talata da dare.
Kazalika, har yanzu ‘yan bindigar da suka kai hari kan jirgin ƙasa na Kaduna-Abuja na riƙe da gwamman matafiyan da suka yi garkuwa da su, inda suke neman gwamnatin Buhari ta biya musu “buƙatunsu”.
“Kundin tsarin mulkinmu ya tanadi yadda shugabanninmu za su sauka daga mulki idan suka gaza ko kuma saboda wani dalili na ƙashin-kai,” in ji NEF. “Loƙaci ya yi da ya kamata Buhari ya fara tunanin wannan zaɓin.”