Injinan Wutar lantarkin Najeriya sun durkushe zuwa 0 Megawatt kaf misalin karfe 10:51 na safiyar Litnin, 26 ga watan Satumba, 2022, rahoton Daily Trust.
Hakan ya sabbaba rashin lantarkin da ake fama da shi a fadin Najeriya.
A bisa bayanan da aka samu, tashar raba wutar lantarkin TCN Afam IV kadai ke aiki amma babu wuta ko daya.
Kamfanonin raba lantarki (DisCos) sun sanar da kwastamominsu bisa aukuwar wannan lamari.
Misalin jami’in yada labaran kamfanin lantarkin Enugu EEDC yace a fadin tarayya ake fama da matsalar rashin wutan.
A cewarsa: “Kamfanin raba wutar lantarkin Enugu (EEDC) na sanar da kwastamominta cewa lalacewar wutan da ya auku misalin karfe 10:51 na safiyar yau, 26 ga Satumba, 2022, ya yi sanadiyar dauke wutan da ake fama da shi a fadin tarayya.”
Hakazalika kamfanin wutan Benin BEDC ya sanar da mazauna yankin Edo, Delta, Ekiti, Ondo da kewaye.
A wani labarin na daban harkar Musulunci a Najeriya ta sanar da cewa: Muzaharar Arbaeen ta bana a Najeriya ita ce muzaharar lumana ta farko ba tare da tashin hankali da rikici daga hukumomin tsaron kasar ba tun shekara ta 2015.
Kamfanin Dillanci Labarai Na Ahlul-Baiti (A.S) – ABNA – A cewar wakilin Harkar Musulunci a Najeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce: Muzaharar Arbaeen ta bana a Najeriya ita ce muzaharar lumana ta farko ba tare da tashin hankali da rikici daga hukumomin tsaron kasar ba tun shekara ta 2015.
A cikin bayanin Dr. Dauda Nalado Memba a Harkar Musulunci a Najeriya, ya bayyana cewa Imam Hussain (AS) ya yi shahada a Karbala a ranar Ashura, 10 ga watan Muharram, watan farko shekara ta 61 bayan hijira. , wanda yayi daidai da 10 ga Oktoba, 680.
Daya daga cikin manufofin Arbaeen shi ne tunawa da irin wahalhalun da Ahlul Baiti na Manzon Allah (S.A.W) suka sha, wadanda aka ja daga Karbala zuwa Dimashk Siriya da kafafuwa ba tare da takalmi ba, a cikin tsananin zafin Saharar Larabawa.
Wannan lamari ne mai ban tausayi wanda ya nuna a fili alamar zalunci ga iyalan gidan manzon Allah (SAW).
Tun daga wannan lokacin ne ‘yan Shi’a da masu zaman makoki ke ta taho daga sassa daban-daban na kasar Iraki zuwa hubbaren Imam Hussain (AS) da ke Karbala a ranar Arba’in.
Musulmi da wadanda ba musulmi ba daga kowane bangare na rayuwa da kuma daga ko ina a duniya suna halartar wannan tafiya.
A kan hanyar su ta zuwa Karbala, masu aikin sa kai suna rarraba abinci da abin sha kyauta ga wadanda suke wannan tafiya, tare da samar da wuraren hutawa, wanka, da kuma barci, yayin da dinbin jama’a ke kan hanyarsu ta zuwa Karbala.
Ya kara da cewa: A yanzu taron na Arbaeen ya kasance mafi girma a duniya kuma yana karuwa duk shekara.
Miliyoyin al’umma daga kasashe daban-daban da kuma daga Najeriya, domin amsa kiran Imam Zaman (A.S) sun hallara a birnin Karbala suna bayyana soyayyarsu da tausayawa da kuma goyon bayansu ga Annabi Muhammad (SAW) da iyalansa cikin wannan musiba.
Ya zo a cikin wannan bayani cewa: Soyayyar da masu juyayi suke nunawa Imam Husaini As da kuma sadaukarwar da mutanen Iraki suka yi musu na nuni da wani abu da dan’adam ke matukar bukata.
Soyayya da sadaukarwa za su haifar da zaman tare cikin lumana da samar da dawwamammen zaman lafiya da adalci da gaskiya a dukkan sassan duniya.
“Imam Husaini (AS) ya sadaukar da rayuwarsa ya kuma yaki azzalumin shugaba Yazid bin Muawiyah.
Shi da iyalansa da wasu da dama daga cikin sahabbansa, dakarun Ibn Ziyad sun kewaye shi, suka yi shahadantar da su a filin Karbala.
Bayan sun fuskanci azabtarwa ta hankali da jiki inda ka hana su ruwan sha na kwanaki.