Wata zakanya na mayar da kumari a gidan kula da namun dawa na Sudan.
Wata zakanya da aka taba wallafa hotunanta yayin da ta ke fama da rashin lafiya da yunwa a gidan kula da namun dawa na al-Quraishi da ke Khartoum, babban birnin kasar Sudan.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce zakanyar mai suna Kandaka na cikin zakuna biyar da ke fama da karancin abinci da cututtuka – kuma biyu cikinsu sun mutu daga baya.
An mayar da sauran zakunan da suka tsira da rayukansu zuwa gandun namun daji na al-Bageir da ke kudu maso gabashin Khartoum.
Wanna sunan na Kandaka, a tarihi akan sanya wa sarauniyoyin tsohuwar masarautar Nuba ne dubban shekaru da suka gabata, kuma a shekarun yanzu sunan ya dawo inda ake sanya wa mata masu fafutukar kare hakin dan Adam – wadanda suka taimaka aka hambarar da gwamnatin tsohon shugaba Omar al-Bashir kamar yadda AFP ta sanar.