Wani rahoton da ke fitowa daga jihar Zmafara ya bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga sun hallaka wani lauya mai suna B.T. Azza Esq.
Abokan aikin sa sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma yi kira ga jami’an tsaro su yi bincike don gano makashin abokin su.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sake jaddada manufarta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wasu miygun ‘yan bindiga sun bindige lauya a birnin Gusau na jihar Zamfara a ranar Alhamis din da ta gabata.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa, wasu ‘yan bindigan sun shiga gidan Barista Benedict Azza da ke unguwar Saminaka, a Gusau, inda suka yi yunkurin sace shi.
Majiya ta bayyana cewa, an lauyan ya yi gwagwarmayar shiga motarsa da nufin ya tsere, amma ‘yan bindiga suka harbe shi har sau uku.
Barrista Junaidu Abubakar, na kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a 19 ga watan Agusta.
Abokin sa ya ba da labarin yadda aka kashe shi Junaidu ya ce, an tsinci ganwar Barista ne a kusa ofishin jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa da ke kan titin bye-pass bayan tsagerun suka hallaka shi, rahoton jaridar Guardian.
A cewarsa: “Jiya da misalin karfe 12:30 na dare, ina gidana naga kiran wasu abokan aikinmu uku suna sanar da ni cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe B.T. Azza Esq, kuma ga can gawarsa a kwance a bakin titi a hanyar bye-pass kusa da ofishin FRSC da ke Gusau.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara.
SP Mohammed Shehu, ya shaidawa majiyar cewa yanzu dai ana ta bincike don gano tushen mutuwar Barista.
Source: LEGITHAUSA