Wasu shugabannin kabilun Fulani sun yi zama a Abuja, sun ce ‘dan takaransu shi ne Bola Tinubu Jagororin kabilar za su goyi bayan jam’iyyyar APC a zaben shugaban kasa, sun ba Tinubu sarauta.
A madadin sauran shugabannin, Ardo Aliyu Liman Bobboi ya ce mutanensu za su zabi APC a 2023.
Jagorori da shugabannin kauyukan Fulani wadanda aka fi sani da Ardo sun yi mubaya’a ga Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zabe mai zuwa.
Daily Trust ta ce wadannan Ardo dabam-dabam da ke karkashin kungiyar Fulbe United for Peace & Development su na goyon bayan jam’iyyar APC.
An kafa wannan kungiya ne domin neman zaman lafiya da hadin-kan Fulani a Najeriya.
Daya daga cikin Hadiman ‘dan takaran, Abdulaziz Abdulaziz ya fitar da wani jawabi na musamman, ya ce Bola Tinubu ya samu goyon bayan Ardo.
Malam Abdulaziz Abdulaziz wanda shi ne mai taimakawa ‘dan takaran wajen yada labarai da hulda da jama’a ya ce Ardon sun yi zamansu ne a Abuja.
A wajen wannan taro aka ji jagororin kabilar ta Fulani su na cewa sun gamsu da Tinubu, ganin abubuwan da ya yi a baya da tsarin da yake da shi. Wasu Fulani a Jeji.
The Nation ta ce an yi zaman ne da hadin-kai da goyon bayan kungiyar Arewa New Agenda wanda tayi alkawarin za ta kawowa APC kuri’u a zaben bana.
Arewa New Agenda ta ce tana da ‘ya ‘ya fiye da 33, 000 kuma za su goyi bayan Tinubu.
Za a rabawa Fulani goron goyon baya Da yake yi wa jama’a bayani bayan an raba goro wajen taron, Ardo Aliyu Liman Bobboi ya ce sakon da za a tafi da shi, shi ne kowa marawa Tinubu baya.
Liman Bobboi ya ce sauran takwarorinsa sun gamsu idan tsohon Gwamnan na Legas ya zama shugaban kasa, za a ga cigaba ta fuskar jagoranci a kasa.
Kungiyar ta kuma bada sarautar Barkindo ga Bola Tinubu, ta na sa rai mulkinsa ya taimaki kabilarsu. Tinubu ya cece mu – Nyako.
A wani rahoto, Sanata Abdulaziz H. Nyako ya ce da aka tsige ubansuwatau Murtala Haruna Nyako daga kujerar Gwamna, Bola Tinubu ne ya yi masa rana.
An fahimci Bola Tinubu ya yi kutun-kutun har Murtala Nyako ya tsere zuwa Landan a shekarar 2014 da gwamnatin Goodluck Jonathan ta taso shi a gaba.