Wasu na kira na Jubril ɗan Sudan ne don su kawar da hankalin gwamnatinmu – Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce iƙirarin da wasu ke yaɗawa cewa wani mutum ne mai suna Jubril daga Sudan yake mulkin Najeriya ba abin dariya ba ne kuma an ƙirƙire shi ne don kawar da hankalin gwamnatinsa.
Buhari ya bayyana haka ne cikin wani fim kan rayuwarsa da aka haska yayin bikin cikarsa shekara 80 da haihuwa na musamman da aka yi a Abuja.
Shugaban na mayar da martani ne ga wani shaci-faɗin da aka fara yaɗawa daf da ƙarewar wa’adinsa na farko a kan mulki cewa ya rasu amma wani mutum mai suna Jubril daga Sudan ne ya maye gurbinsa a Fadar Shugaban Ƙasa Aso Rock.
Ya ce masu ta da zaune tsaye ne suka ƙirƙiri maganar “saboda wulaƙanci”.
A cewarsa: “A’a, ba abin dariya ba ne saboda waɗanda suka ƙirƙiri zancen sun yi ne saboda wulaƙanci. Suna so su karkatar da hankalin gwamnati daga kan muhimman abubuwa.
“Babbar manufarmu ita ce yin ayyukan raya ƙasa, mu fargar da mutane su san cewa akwai buƙatar su yi aiki tuƙuru don su rayu cikin walwala.
“Suna [masu yaɗa iƙirarin] son su ji daɗin rayuwa ne kawai da kuma samun goyon bayan al’ummarsu.”