Wasu Daga Cikin Kungiyoyin Malaman Jamai’oi A Najeriya Sun Dakatar Da yajin Aiki Da Suke yi.
Ƙungiyoyin ma’aikata biyu na jami’o’in gwamnati a Najeriya NASU da SSANU sun sanar da janye yajin aikin da suke yi na watanni biyu bayan ganawarsu da Ministan Ilimi Adamu Adamu a jiya Asabar.
Kwamatin hadin gwiwa da Kungiyoyin Senior Staff Association of Nigerian Universities da Non-Academic Staff Union of Educational and Allied Institutions suka kafa ne ya gana da ministan a Abuja.
Sai dai azuzuwan jami’o’in za su ci gaba da kasancewa a rufe saboda Kungiyar malaman jami’a ta Kasa ASUU taki yarda ta janye yajin aikin da ta shafe fiye da wata biyar tana yi.
Kungiyoyin biyu Na NASU da SSANU sun fara nasu yajin aikin ne a watan Maris jim kadan bayan da ASUU ta fara nata.
READ MORE : Kasar Iran Za ta Fara Hako Man Fetur A Rijiyoyin Da Suke Hadaka Da Kasar Saudiya.
Ana sa bangaren Shugaban Kungiyar SSANU, Mohammed Haruna Ibrahim, ya fadi cewa jingine yajin aikin da suka yin a watanni biyu ne kawai, domin bawa gwamnati damar aiwatar da alkawuran da ta yi musu.
READ MORE : Jami’an Sojin Ruwan Najeriya Sun Damke Jirgin kasar Norway Yana Satar Danyen Man Najeriya.