Wani binciken jaridar Punch ya ce kokarin da kwamitin sulhu na jam’iyyar APC ke yi na sasanta rikicin cikin gida a wasu jahohin jam’iyyar na fuskantar koma baya a wasu jihohi.
Tun a watan Yunin 2020 da aka kaddamar da kwamitin karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, an ɗage taron sau da dama.
Rikicin ana ganin ya fi kamari a wasu jihohi kamar Osun, tsakanin gwamna Oyetola and ministan harkokin cikin gida na Najeriya Rauf Aregbesola, wanda ya kai ga ɗage zaɓen shugabannin jam’iyyar na jihar.
A Kwara kuwa har yanzu an gaza shaw kan gwamnan jihar AbdulRahman AbdulRazaq da kuma ɓagaren ministan watsa labaai na Najeiya Lai Muhammad.
A jihar Kano ma ana ci gaba da takaddama tsakanin tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma na tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau, inda ko wanne ɓangare ke cewa shugabancinsa ne sahihi.
Haka abun yake a Zamfara ma, inda ɓangaren tsohon gwamnan jihar Abdulazizu Yari ya hae da na Kabiru Marafa, suk kuma ƙalubalantar jagorancin gwamna Matawalle wanda ya koma jam’iyyar a baya bayan nan.
A makwabciyarta ma jihar Kebbi ana ci gaba da taƙaddama tsakanin ɓangaren gwamnan jihar Abubaka Atiku Bagudu da kuma na tsoon gwamna Adamu Alieo, wanda suka bue sabon ofishin jam’iyyar kwanan nan.
Alamu dai na nuni da cewa za a yi babban taron jam’iyyar ba tare da an sasanta wadannan bangarori ba, yayin da shi kansa kwamitin sulhun ke kokarin kammala aikinsa kwanan nan.