Wani Jirgin Sojin Saman Najeriya, Ya Kashe Yara 7 Bisa Kuskure A Nijar.
Hukumomin a jihar Maradi dake Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar yara bakwai sakamakon wani hari bisa kuskure da wani jirgin sojin saman Najeriya ya kai a iyaka da jihar.
Da yake tabbatar hakan ga kamfanin dilancin labaren AFP, gwamnan jihar Maradin Malam Chaïbou Aboubacar, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da ta gabata a kauyen Nachadé, dake kusa da iyaka da tarayyar Najeriya.
Ya ce harin bisa kuskure ya rusa da yara 12, cikinsu bakwai sun mutu sai kuma biyar da suka raunana.
Lamarin kuma ya faru ne a lokacin da sojojin saman Najeriyar ke kai hare haren kan ‘yan bindiga a yankin.