Wani Hari Ya Yi Ajalin Sojin Burkina Faso 12.
Rundinar sojin Burkina Faso, ta sanar da mutuwar sojinta 12 da kuma wasu ‘yan sa kai hudu a wani hari da ta ce na mayakan jihadi ne a arewacin kasar.
Harin na ranar Juma’a an kai shi ne kan wani barikin soji dake yankin Namissiguima, inda kuma sojoji 21 suka jikkata.
Wata majiya a yankin ta shaidawa masu aiko da rahotanni cewa harin mayakan na maida martani ne kan wani hari da sojojin kasar suka kai a yankin inda suka hallaka gomman ‘yan ta’adda a makon da ya gabata.
Kamar makobtan Mali da Nijar, Burkina faso ta fuskantar hare hare daga mayakan dake ikirari da sunan jihadi tun cikin shekarar 2015.
Tun lokacin Hare haren da ake dangatawa da na reshen Al’Qaida da kuma IS, sun yi sanadin mutuwar mutum sama da 2,000 da kuma tilastawa wasu miliyan 1,8 kaura.
READ MORE : Saudiyya Ta Lamunce Mutum Miliyan Daya Su Yi Aikin Hajji A Bana.
A makon da ya gabata dai sabon shugaban kasar, Laftana Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya sanar da kafa wani kwamiti domin tattaunawa da gungun mayakan dake ikirari da sunan jihadi domin kawo karshen zubar da jini.
READ MORE : Ɗan majalisar Najeriya na son a fara ɗaure ‘yan daudu ko tarar N500,000.