Wani Dan Bindiga Da Ba’asan Ko Waye Ba Ya Harbe wani Bayahude A Gabar Yammacin Kogin Jodan.
Kakakin sojojin Isra’ila ya bayyana cewa wasu yan bindiga da ba’asan ko su waye ba sun kutsa kai a wajen da sojoji suka kafa shingaye a mashigar gidajen yahudawa yan share wuri zauna inda suka harbe mai gadin wajen
Wasu rahotanni sun bayyana cewa hotunan da kamaran jamian tsaro ya dauka a yankin yanuna cewa maharan sun sauka daga mutarsu da suka ajiye acan baya, inda suka dira a ofishin masu gadi suka bude musu wuta kafin daga bisani suka tsere kamar yadda jaridar Times ta Israela ta bayyana
Lokacin da jami’an tsaron Isra’ila suka isa wajen da abin ya faru sun samu wani mutum mai shakaru 20 a sume yaji mummuna rauni sakamakon Harbin sa da aka yi da bindiga , inda ko numfashi baya yi, dakarun na isra’ila sun gudanar da bincike ko za su iya ganin wadanda suka kai harin. Tare da rufe mashaigar garin Salfit dake arewacin rukunin gidajen da abin ya faru
Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya sanar da alhakin kai wannan gari na jarumta, wannan yana zuwa ne bayan da sojojin Isra’ila suka tsannata kai hari a masallacin Quds mai tsarki da hakan yayi sanadiyar jikkata da shahdar falasdinawa da dama, da kuma kashe akalla yahudawa 14 a hare hare daban daban.