Wani Abu Da AKe kyautata Zaton Bam ne Ya fashe A Wata Mashaya A Najeriya.
Rahotanni daga garin Kabba na Jihar Kogi ta arewa maso tsakiyar Najeriya na cewa wani abu da mai karfi ya fashe a wata mashaya da ake kyautata zaton zargi bam ne . Sai dai bayanan farko-farko da aka samu bayan faruwar lamarin lamarin da misalin karfe tara da minti 15 na daren Lahadi, ya nuna cewa ba bu asaarar rayuka da aka samu a fashewar.
Lamarin wanda ya faru ne a wata mashaya ta Omofemi a unguwar Okepadi, da ke garin Kabba, ya yi sanadiyyar lalacewar gini da kujeru da kuma tebura a wurin.
Kakakin ya kara da cewa, tuni kwamishinan ‘yan-sandan jihar Mista Edward Egbuka ya ba da umarnin a tura kwararru a kan warware bam, wurin domin gudanar da bincike don gano musabbabin fashewar da kuma irin illar da aka samu.
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun fashewar wasu abubuwa a wuraren shan barasa a garin na Kaba ba, ko a ranar 11 ga watan Mayu na 2022 ma, wani bam ya tashi , Fashewar wadda ta auku da misalin karfe 10 saura kwata na dare a wancan lokacin, rahotanni sun ce ta yi sanadiyar mutuwar mutum 3, da kuma jikkata wasu da dama.
Idan ana iya tunawa a baya-bayan nan an samu irin wannan fashewar a wasu gidajen shan barasa a arewacin Najeriya, a jihohin Yobe da kuma Kaduna.