Wakilan Majalisar Dattawan Najeriya za su gana da Sanata Ekweremadu a kurkukun Landan.
Majalisar Dattawan Najeriya ta ce za ta tura wakilanta zuwa birnin Landan na Birtaniya don ganawa da tsohon mataimakin shugaban majalisar, Sanata Ike Ekweremadu, wanda ake tsare da shi bisa zargin yunƙurin cire wa wani matashi ƙoda.
Shugaban Majalisa Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Laraba, yana mai cewa za su taimaka wa abokin nasu ta hanyar sama masa lauoyoyi.
“Wakilai daga Kwamtin Harokokin Waje na Majalisa zai tafi Landan nan da kwana biyu saboda hakan,” a cewarsa. “Kuma mun umarci kwamatin ya tattauna da ofishin jakadancin Birtaniya a Birtaniya.”
Ahmad Lawan ya ƙara da cewa ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya ya yi ƙoƙari wajen haɗa su da Sanata Ike da kuma samar masa lauyoyin da za su kare shi a gaban kotu.
A makon da ya gabata ne wata kotun majistare ta umarci a kai sanatan gidan yari bayan ‘yan sanda sun tuhume shi da kai wani matashi Birtaniya da zummar cire masa ƙoda.
Sai dai Ekweremadu ya ce an kai shi ne don ya bai wa ‘yarsa taimakon ƙoda kuma ba tilasta masa aka yi ba.
A ranar 7 ga watan Yuli za a ci gaba da sauraron ƙarar.