Wahalar fetur da matsalar wutar lantarki a Najeriya.
An shafe kwanaki ana fuskantar wahalar fetur a Najeriya bayan gano wani gurbataccen man fetur da aka shigar da shi, wanda daga baya gwamnatin kasarta dauki matakin janye shi, sai dai tun daga wannan lokaci ne ake ci gaba da ganin dogayen layukan motoci a gidajen mai da ke fadin kasar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar matsanancin karancin wutar lantarki a fadin kasar.
A farkon makon nan kamfanonin rarraba wutar lantarki sun fitar da sakonni neman afuwa bisa yawaitar katsewar wutar lantarkin, wanda hakan acewarsu ta faru ne sanadiyar yankewar karfin wutar daga tashohin samar da wutar lantarki na kasar.
Har wa yau hakan na faruwa ne a lokacin da farashin tikitin jiragen sama suka yi tashin gwauran zabi a kasar, wani abu da aka ta’allaka da karancin man jirgi Jet A1, inda har aka shiga fargabar cewa kamfanonin jiragen saman za su iya dakatar da ayyukansu baki daya.
READ MORE : Sheikh Ibrahim Zakzaky; Jami’an tsaron Najeriya sun bukaci matata ta cire kayan jikinta.
Shin mene ne ya haifar da wadannan matsaloli? Ta yaya za a iya shawo kansu?
A yaushe ne ake sa ran za a samu saukin su? Wadannan ne abubuwan da aka tattauna a filin Ra’ayin Riga.