An yanke wa sanannen wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume, hukuncin daurin shekara bakwai a gidan yari.
Mai shari’a Binta Nyako, ta samu Wadume da laifin tserewa daga hannun hukuma da kuma yin mu’amala da muggan makamai ba bisa ka’ida ba.
Yang Jiechi Ya Halarci Bikin Bude Baje Kolin Kasa Da Kasa Na Hanyar Siliki Karo Na Shida Tare Da Gabatar Da Jawabi
Mai shari’a Nyako ta kuma yanke wa Rayyanu Abdul hukuncin daurin shekara uku saboda ya ajiye Wadume a gidansa da ke Kano bayan Wadume ya tsere daga hannun ‘yan sanda a Ibi.
Alkalin kotun ta soke tuhuma ta daga, inda ake tuhumar sa da laifin yin garkuwa da Usman Garba wanda aka fi sani da Mayo da kuma karbar Naira miliyan 106 kafin a sake shi.
Mai shari’a Nyako, ta yanke hukuncin ne a ranar 22 ga watan Yulin bana.
A halin yanzu Najeriya na fama da matsanancin rashin tsaro sakamakon ‘yan garkuwa da mutane masu sace mutane su bukaci kudin fansa.
Gwamnatin Shugaba buhari wacce ya rage mata ‘yan watanni ta sauka Tayi alkawarin kawo karshen matsalar rashin tsaro amma har yanzu babu sassauci a lamarin matsalar rashin tsaron a yankuna mabambanta na fadin Najeriya.
Fatan al’ummar Najeriya shine a samu yanayin da wannan bakuwar matsala da aka samu Kai a ciki zata gushe domin samun ingattaciyar rayuwa ga ‘yan Kasa.
Zawarawan kujerar Shugabancin Najeriya daga mabambantan jam’iyyu dai tuni suka yima al’ummar Najeriya alkawarin kawo karshen matsalar idan aka kada musu kuri’a Amma mutane na tsoron kwada ‘yan gidan jiya.
Source: Leadership