Kawo yanzu mutanen Najeriya sun san ‘yan siyasan da suke neman zama shugaban kasa a 2023 Duka manyan ‘yan takaran da ake da su, su na da iyali, daga cikinsu har da mai mata fiye da daya.
Atiku Abubakar ne ya fi kowa iyali, shi kuwa ‘Dan takaran APC, Bola Tinubu yana auren Fasto ne.
A wannan rahoto da ya fara bayyana a jaridar Daily Trust, an tattaro bayani ne a game da matan masu neman zama shugaban kasa a zabe mai zuwa.
A cikin wadannan ‘yan takara da ake da su ne za a samu shugaban kasa. Hakan yana nufin tsakanin wadannan mata za a samu uwargidar Najeriya.
Ga su nan kamar haka: 1. Amina Titilayo Atiku Abubakar ta na da kishiyoyi.
Amina Titilayo wanda aka fi sani da Titi Atiku Abubakar ita ce Uwargidar ‘dan takaran PDP, Atiku Abubakar. Asalinta mutumiyar Osun ce da aka haifa a Legas.
Tsakanin 1999 da 2007, Titi Abubakar ta na Aso Villa a lokacin mai gidanta yana mataimakin shugaban kasa.
Tun 1971 ta auri Atiku lokacin yana aikin Kwatsam.
Bugu da kari, Titi ta samu satifiket wajen kula da otel a Scuola International de Science Turistiche a ketare.
Mai dakin ‘dan takaran ta na da lambar yabo iri-iri. 2. Fasto Remi Tinubu – Uwargidar kuma Sanata Sanara Oluremi Tinubu ita ce Mai dakin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Ita ma dai an haife ta ne a Legas a shekarar 1960, amma iyayenta mutanen jihar Ogun ne.
Tinubu ta kammala sakandare a Our Lady of Apostles Secondary School, Ijebu-Ode a 1979, ta na da Difloma a makarantar cocin Redeemed Christian Bible College.
Rahoton ya nuna uwargidar ‘dan takaran na jam’iyyar APC ta yi Digiri a bangaren ilmin tsirrari daga Jami’ar Ife da kuma shaidar NCE a kwalejin ilmi na Adeyemi.
Sanatar ta zama uwargidar jihar Legas a lokacin da mai gidan ta ya yi gwamna na shekaru takwas. Tinubu za ta sauka daga kujerar Sanata a 2023 bayan shekaru 12.
Matan Yan takaran 2023 Hoto: Pulse, Newswirengr, Info Nigeria Asali: UGC 3. Margaret Obi – Sahibar Peter Obi Asalin sunanta kafin aure shi ne Margaret Brownson Usen.
A shekarar 1992 ta auri Peter Obi, kuma su ka haifi ‘ya ‘ya biyu. Iyayen ta mutanen jihar Kuros Riba ne.
Margaret Obi ta taka rawar gani a lokacin da Peter Obi yake gwamna a Anambra, ta yi kokari wajen ganin an ba mata mukamai sosai a gwamnatin mai gidanta.
A dalilin Margaret Obi ne ma’aikatar mata da cigaban al’umman jihar Anambra ta kafa kotu na musamman domin sauraron karar cin zarafin mata da kananan yara.
4. Ba a jin duriyar Salamatu Kwankwaso Wanda za a iya cewa Duniya ba ta santa ba a jerin wadannan manya mata ita ce Hajiya Salamatu Musa Kwankwaso, mai dakin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Uwargidar Rabiu Musa Kwankwaso wanda yake neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, boyayya ce a cikin matan manyan ‘yan siyasan da ke kasar nan.
Hajiya Salamatu Kwankwaso diya ce a wurin Alhaji Murtala Sule Garo. Daga cikin ‘yan ‘yansa akwai ‘yan siyasa – Murtala Sule Garo, da Hon. Nasiru Sule Garo.
A lokacin da mai gidanta yake gwamna a jihar Kano, ba a ji duriyarta ba. Har Kwankwaso ya sauka daga mulki, ba a ji labarin ofishin uwargidar gwamna ba.
Legit.ng Hausa ta fahimci Hajiya Salamatu ita ce mata ta biyu da Kwankwaso ya aura. Ita ta fara karatunta ne a makarantar sakandaren nan na GGSS Kabo a Kano.
Zargi ya dabaibaye ‘yan takara Ku na da labari a 1993 an taba kai Bola Tinubu kotu bisa zargin alaka da kudin harkar kwayoyi.
Sannan an taba zargin Atiku Abubakar da boye $40m a Amurka. Sai dai Alhaji Atiku Abubakar ya na ikirarin ya yi arziki ne tun a gidan kwastam, shi ma Bola Tinubu na APC yana cewa kafin ya shiga siyasa ya zama Attajiri.