Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNNP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alkawarin mai da wa’adin jarrabawar UTME ta JAMB ta zama shekaru hudu idan ya gaji Buhari.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da tutar jam’iyyar NNPP ga ‘yan takarar gwamna a jihohin Arewa maso Gabas shida da kuma na sanata 18 a ranar Alhamis a jihar Bauchi.
Ya bayyana cewa, akwai dalibai da yawa da ke samun sakamako mai kyau na JAMB, amma ba sa samun damar samun gurbin karatu a shekarar sabida wasu dalilai.
Dalibai suna kokari, amma babu gurbin shiga jami’a Ya ce idan haka ta faru ba laifinsu bane, don haka gwamnati za ta zo da hanyar share musu hawaye kowa ma ya huta.
A cewarsa: “Ana kakabawa wadannan daliban da iyayensu kudi domin sake rubuta jarrabawa a duk shekara amma idan aka zabe mu za su mai da wa’adin JAMB ya zama shekaru hudu.”
“Za mu ba da wa’adin shekaru hudu ga JAMB domin ‘ya’yanmu su yi amfani da sakamakon jarrabawar su samu gurbin karatu a manyan makarantu a wannan lokacin.”
Dan takarar ya kuma yi alkawarin bayar da fom din neman gurbin shiga jami’a da kuma na neman aiki kyauta ba da kudi ba.
A cewarsa: “Za mu inganta tare da fadada jami’o’inmu, kwalejin fasaha da kuma kwalejin ilimi kuma mu habaka ingancinsu su yi gogagga da duniya. ”
Gwamnatina za ta gina ajujuwa 500,000 a fadin kasar, domin daukar yaran da ba sa zuwa makaranta sama da miliyan 20 a saka su a makaranta.
“Za mu sanya dukkan jarrabawar WASC, NECO, NABTEB, NBAIS, JAMB da sauransu duk su zama kyauta.”
Su waye ‘yan takarar NNPP a jihohin Arewa maso Gabas?
Kwankwaso ya ce dukkan ‘yan takarar gwamnan NNPP a Arewa maso Gabas sun cancanta,, kuma za su iya samar da mulki na gari ga al’ummar jihohinsu.
‘Yan takarar NNPP na gwamna a yankin sun hada da Sa’adu Tahir na jihar Adamawa, Sanata Haliru Jika na jihar Bauchi, da Dr Umar Alkali na jihar Borno.
Hakazalika, akwai Muhammad Mailantarki na jihar Gombe, Yahaya Sani a jihar Taraba da kuma Umar Alhaii a jihar Yobe.
Da yake magana, dan takarar gwamnan jihar Bauchi, Sanata Jika ya bukaci magoya bayansa da su kasance masu amana da jajircewa, kuma su ba NNPP sama har kasa dodar dukkan kuri’unsu.