UNECA Yarjejeniyar AfCFTA Za Ta Habaka Al’amuran Sufuri A Africa.
Hukumar kula da tattalin arzikin nahiyar Afrika ta MDD (UNECA), ta ce ana sa ran yarjejeniyar ciniki marar shinge ta nahiyar Afrika AfCFTA, za ta kara habaka al’amuran sufuri tsakanin kasashen nahiyar da kusan kaso 50.
Hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, bangaren sufuri na nahiyar zai matukar amfana daga yarjejeniyar, tana mai cewa, kiyasin da aka yi a baya-bayan nan mai taken “tasirin yarjejeniyar ciniki marar shinge ta nahiyar kan bukatar sufuri da ababen more rayuwa”, ya nuna cewa, sama da kaso 25 na ribar da za a samu daga cinikayya tsakanin kasashen, zai tafi ne ga bangaren sufuri kadai, kuma kusan kaso 40 na karuwar hidimomin a nahiyar zai tafi ga bangaren.
Ta ce nazarin da masana na bangaren makamashi da ababen more rayuwa da hidimomi na hukumar suka yi, ya bayyana damarmakin zuba jari a bangaren na sufuri.