An umarci wani matashi da ya share harabar kotu bisa laifin satar turare a wani kantin siyayya a Abuja.
Mai shari’a Malam Ishaq Hassan ya hukunta matashin ne bayan da ya amsa aikata laifin tare da yi masa gargadi.
Ba wannan ne karon farko da ake yiwa matasa hukunci mai ban mamaki irin wannan ba a Najeriya bisa aikata kananan laifuka.
Wani alkali, Malam Ishaq Hassan a ranar Talata ya umarci wani matashi mai shekaru 24, Valentine Nmoye da ya ya share harabar kotun Karu a Abuja na tsawon sa’o’i uku bisa laifin satar turaren N4,000 daga wani kantin siyayya.
Hassan ya ba da wannan umarnin ne yayin da matashin ya amsa laifinsa na sata, ya kuma gargadi matashin da ya daina aikata mummunar dabi’ar sata, rahoton Punch.
A Kasuwar Singer Ta Kano A tun farko, dan sanda mai shigar da kara, Olarewaju Osho ya shaidawa kotun cewa, Sadiq Ahmed na Tahalid Stores da ke Garki a Abuja ya kai karar matashin ga ofishin ‘yan sandan Garki.
Osho ya bayyana cewa, an zargi matashin ne da laifin shiga kantin ne tare da sace turare guda uku da kudinsu ya kai N4,000.
Yayin bincike, Osho ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin da ya aikata. Ya ce abin da ya aikata laifin a dokar Panel Code sashe 287.
Source:LEGITHAUSA