Tuwo na fara nema bayan dawowa gida daga Sudan- Ɗaliba.
Fatima Sanusi ɗaliba ce da ke karatu a wata jami’a da ke ƙasar Sudan, ta bayyana yadda ta ji, bayan dawowa gida tare da haɗuwa da iyayenta.
Ɗalibar, wadda ke shekara ta huɗu a karatunta na likitar haƙora na daga cikin ɗaliban da suka koma Najeriya ta ƙasar Masar, bayan da yaƙi ya ɓarke tsakanin ɓangarorin soji biyu a Khartoum, babban birnin Sudan.
A tattaunawarta da BBC jim-kaɗan bayan isarta Kano, Fatima ta bayyana halin da ta tsinci kanta a ƙasar ta Sudan.
Ta ce “na sharɓi kukan murna bayan da na ga iyalina domin na zata mutuwa zan yi a Sudan saboda irin abubuwan da ke faruwa.”
Daga nan kuma sai ta buƙaci a ba ta abincin da take matuƙar kewa.
Ta ce “Tuwo na fara nema saboda ina marmarinsa sosai.”
Fatima ta ce a yanzu ba ta fara tunanin komawa Sudan ba duk da cewa shekara ɗaya ta rage mata a karatun nata.
“A yanzu ban fara tunanin komawa ba har sai komai ya lafa.”
“A Khartoum wurin da muke kwana yana kusa da barikin soja, wannan ya sanya mu cikin haɗari.”
“Akwai wani lokaci da sojojin suka zo inda muke suka ce kowa ya kwanta, a wannan lokacin na yi tunanin cewa duk mutuwa za mu yi.”
‘Idan faɗan ya ƙi ƙarewa zan nemi a tura min sakamakon jarrabawar ƴata’
Mahaifin Fatima, Sanusi Musa wanda ya bayyana farin cikinsa kan komawar ƴarsa gida, jihar Kano, ya ce zai tsaya ya ga yadda lamura za su kasance.
“Yanzu za mu jira mu ga yadda abubuwan za su kasance, idan yaƙin ya ƙare suka kira, za ta koma ta kammala karatunta tun da shekara ɗaya ta rage mata”, in ji shi.
“Amma idan yaƙin ya ja lokaci za mu buƙaci makarantar da take karatu su tura mana da sakamakon jarrabawarta domin ta je wata makarantar ta ƙarisa karatun nata.”
Mahaifin na Fatima ya ce shi da mahaifiyarta ba sa iya yin bacci bayan da yaƙin na Sudan ya ɓarke.
“A lokacin da muka yi magana da ita ta waya ta shaida mana abubuwan da ke faruwa sai lamarin ya ƙara dagule mana saboda tunanin ta muke yi a kodayaushe.”
“Na ji daɗi sosai da ta dawo gida.”
Najeriya dai ba ta samu damar fara kwaso ɗalibanta da ke karatu a Sudan kan lokaci ba bayan ɓarkewar faɗan, wani abu da ya janyo wa gwamnati suka a cikin gida.
Faɗa ya ɓarke ne tsakanin dakarun gwamnatin Sudan ƙarƙashin jagorancin shugaban gwamnatin sojin ƙasar Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa kuma jagoran rundunar tsaron kar-ta-kwana da ake yi wa laƙabi da RSF, Janar Mohamed Hamdan Dagalo.
Yanzu haka dai ana ci gaba da tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu masu faɗa da juna domin ganin yadda za a kawo sulhu.
Sai dai duk wani yunƙuri na tsagaita wuta a baya bai kai ga nasara ba, ganin cewa koda an samu amincewar ɓangarorin, akan ci gaba da ɓarin wuta bayan ƙanƙanin lokaci.