Tunisia ‘Yansanda Sun Rufe Ofishin Majalisar Koli Ta Alkalan Kasar.
‘Yansanda a kasar Tunisia sun rufe ofishin majalisar koli ta alkalan kasar a jiya Litinin. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa shugaba Kais Saeed ya yi alkawarin cewa ba zai yi shishigi cikin al-amuran alkalanci a kasar ba, amma ya zargi wasu alkalan da goyon bayan jam’iyyun siyasa wadanda suke adawa da shi.
Banda haka ya kara da cewa akwai wasu bara gurbin alkalai wadanda suka yi zurfi cikin cinhanci da rashawa. Shugaba Kais Saied dai ya kwace iko da majalisar dokokin kasar a shekarar da ta gabata ya kuma rufe ta sannan ya kori firai ministan kasar.
Shugaba Sa’id ya mayarwa kansa dukkan ikon zartarwa a kasar, sannan ya ce zai ci gaba da mulki tare da amfani da kirkirarrun dokoki har zuwa lukacinda zai rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar sannan ya bukaci mutane su yi zaben raba gardama a kansa. Kafin shugaba Saeed ya kwace iko dai majalisar dokokinnkasar ta kasa yin kome wajen warware matsalolin mutanen kasar.