Ministar tsare-tsare ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Judith Suminwa Tuluka ta zama mace ta farko da ta zama Firaminista a Afirka.
Masaniyar tattalin arziki da tsimi da dabara, ta karbi mukamin Firaministan ne a ranar Litinin.
Tuluka ta bayyana cewa “Aikin yana da girma, akwai kalubale mai tarin yawa… amma zan sauke nauyin da ya rataya a kaina.
Tuluka ta bayyana cewa “Aikin yana da girma, akwai kalubale mai tarin yawa… amma zan sauke nauyin da ya rataya a kaina.”
Shugaban kasar, Tshisekedi ya yi nasara da kashi 73.47 cikin 100 a kuri’un da aka kada a watan Disamban 2019.
Sai dai ‘yan adawar kasar ba su karbi zaben ba, inda suka ayyana shi a matsayin shirme.
A gefe guda a lokacin zaben, an dakatar da kada kuri’a na tsawon kwana daya sakamakon tashe-tashen hankula da aka samu a rumfunan zabe a kasar.
Jam’iyyun da ke goyon bayan Tshisekedi sun samu fiye da kashi 90 na kujerun majalisar dokokin kasar, wanda hakan ke ba shi damar yin doka cikin sauki.
Za a dora wa sabuwar Firaministan nauyin tafiyar da wasu al’amuran al’ummar kasar mai kimanin mutane miliyan 100.
DUBA NAN: Dan Nasiru El- Rufa’i Ya Maida Martani Ga Gwamna Uba Sani
Tshisekedi, ya zama shugaban kasar a shekarar 2019, inda ya yi alkawarin inganta yanayin rayuwa a Dimokuradiyyar Congo, wacce ke da arzikin ma’adinai.