‘Tuɓe rawanin Wazirin Bauchi ba shi da alaƙa da Atiku Abubakar’
Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa aka cire Wazirin Bauchi, Alhaji Bello Kirfi daga mukaminsa na Waziri.
Gwamnatin ta ce tsohon Wazirin ba ya kama girmansa ne a wuraren da hukuma ba za ta iya zuba masa ido ba.
A ranar Larabar da ta wuce ne fadar jihar Bauchin ta sanar da tuɓe rawanin Wazirin.
Sai dai bangaren Wazirin ya yi zargin cewa gwamnan jihar ne ya saka masa karan-tsana saboda yana goyon bayan dan takarar shugaban ƙasa na jam`iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Hon Abdurrazak Nuhu Zaki, kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautun gargajiya na jihar ya shaida wa BBC, cewa matakin da aka ɗauka sam ba shi da alaƙa da Atiku Abubakar, hasalima, a cewarsa, masu danganta lamarin da ɗan takarar, ƙarya suke.
Ya ce “umarnin da gwamnan jihar Bauchi ya bayar tun da aka fara kamfe, ga duk wani ɗan Jam’iyyar PDP, ya yi tallan Atiku Abubakar, ya kuma yi tallan gwamna,”
Ya ƙara da cewa Gwamnan jihar Bauchi ya kafa kwamiti na tallan ƴan takarar Jam;’iyyar PDP daga sama har ƙasa, “don haka wani ya zo ya ce wai Alhaji Muhammadu Bello Kirfi ya rasa kujerarsa wai saboda taron a tallata Atiku Abubakar, ya yi ƙarya kuma ya yaudari kansa.”
Abin da ya sa gwamnati ta tuɓe rawanin Wazirin Bauchi
Hon Abdurrazak Nuhu Zaki ya ce dalilin da ya sa gwamnati ta ɗauki matakin sauke Wazirin na da nasaba da wasu maganganu da ya yi a lokacin da ɗan takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin PDP ya kai ziyara jihar waɗanda suka nuna cewa kamar an raina fada, an raina Sarki.
Hakan ya faru ne bayan da shi Atiku Abubakar ya gama jawabinsa, kuma gwamna na ƙoƙarin ya mayar da jawabi ne shi Waziri ya nemi a ba shi abin magana, gwamnan kuma ya nemi a bashi, amma sai ya ɓige da wasu maganganu maras daɗi.
“Ba wannan ne karo na farko da aka cire tsohon Wazirin daga matsayin Wazirin Bauchi ba, a baya ma an cire shi, gwamnan jihar Bauchi ne ya je ya bada hakuri, da kansa ya kai masa takardar maishe shi.”
Hon Zaki ya kuma ce kwata-kwata ba bu siyasa a batun, sai dai “muna ƙoƙarin kare darajar gwamnati ne da mutuncinmu,”
“Don haka daga ofishina ne ya zamto abubuwan da ake tafiyarwa muka ga ba su dace ba.” in ji Hon Abdurrazak Nuhu Zaki.