Tsohon shugaban kasan Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya aike wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da wani sako mai daukar hankali.
A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya ya cika shekaru 80 a duniya, jama’ar kasa suna ci gaba da aiko sakwannin gaisuwa.
Goodluck Jonathan ya siffanta shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban da ya yi sa’ar samun rike ragamar kasar nan har sau biyu.
Tsohon shugaban kasan Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya aikewa shugaba Muhammadu Buhari da wani muhimmin sako yayin da yake cika shekaru 80 a duniya.
Buhari ya cika shekaru 80 a yau Asabar 17 ga watan Disamban 2022, an haife shi ne rana mai kamar ta yau a shekarar 1942,
Jaridar PM News ta ruwaito
A cikin wata sanarwa da Jonathan ya fitar, ya taya Buhari murna tare da yi masa addu’o’in fatan alheri yayin da ake ci gaba da rike ragamar Najeriya.
A cikin sakon na fatan alheri, Jonathan ya ce, Buhari na ya samu damar rike ragamar kasar nan har sau biyu; a matsayin shugaban soja da na farar hula, Within Nigeria ta ruwaito.
A cewar tsohon shugaban kasan a wata sanarwa da Ikechukwu Eze, mataimakinsa kan harkokin yada labarai ya fitar:
“Ina farin cikin taya ka murnar bikin cika shekaru 80
Tare da iyalanka, abokai da masu fatan alheri, muna gode wa Allah da ya baka nisan kwana da karfin iya tafiyar da lamurran kasar nan na tsawon shekaru bakwai da rabi.”
Jiga-jigan ‘yan Najeriya da dama sun bayyana fatan alheri ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa cika wadannan shekaru masu yawa. Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hau mulkin Najeriya a 2015 lokacin da ya karbi mulkin a hannun Goodluck Jonathan.
Manyan Zarge-zarge 12 Da Aka Yiwa Shugaban Kasa Saura watanni kadan shugaban kasa Buhari ya sauka a mulkin da ya hau tun 2015, a yau ya cika shekaru 80 a duniya.
Shugaba Buhari ya fuskance maganganu masu daukar hankali da jawo cece-kuce daga magautansa, amma wani jigon APC ya yaba masa.
A cewarsa, shugaba Buhari ya yi niyyar kawo canjin da ya yi alkawarin kawowa a 2015, kuma ya cika alkawari duk da cewa mutane suna ganin ya gaza.