Tsohon Shugaban Kasar Zambia Rupiah Banda Ya Rasu.
A jiya Jumaa ne dai aka sanar da rasuwar tsohon shugaban kasar ta Zambia yana dan shekara 85,bayan da ya yi fama da cutar daji.
Dan mamacin mai suna Andrew Banda ne ya sanar da mutuwar mahafin nashi a birnin Lusaka, kamar yadda kamfanin dillancin labarun AFP ya nakalto.
Rupiah ya kasance shugaban kasar ta Zambia na hudu tun daga samun ‘yancin kasar. Ya yi zangon shugabancin kasar sau hudu wanda ya fara daga 2008. Ya dare kujerar mukin kasar ne dai bayan rasuwar shugaban kasa Mwanwasa da ya kasance mataimakinsa.
An yaba wa zamanin mulkinsa da cigaban tattalin arzikin kasar, da kuma cin hanci da rashawa.
Kasar Chana ta zuba hannun –jari a fagen ma’adanin tagulla da kasar da shi da yawa.
Har ila yau, al’ummar suna tunawa da shi saboda gina manyan hanyoyi, asibitoci da kuma makamrantu.
READ MORE : Rasha Ta Zargi Amurka Da Taimakawa Kasar Ukiran.