Allah Ya yi wa tsohon shugaban rikon kwaryar Najeriya Cif Ernest Shonekan rasuwa kamar yadda rahotanni da dama a kasar suka tabbatar..
Cif Shonekan ya rasu ne a sibiti a birnin Legas ranar Talata kamar yadda rahotannin suka ce.
Tsohon shugaban kasar ya rasu yana da shekara 89 a duniya.
Cif Shonekan ne shugaban gwamnatin rikon kwaryar Najeriya daga tsakanin 26 ga watabn Agusta zuwa 17 ga watan Nuwamban 1993.
Marigayi Janar Sani Abacha wanda yake Sakataren Tsaro na kasar a lokacin shi ne ya hambarar da gwamnatin rikon Cif Shonekan ta ruwan sanyi ba tare das zub da jini ba a Nuwamban 1993.