Sanata Yusuf Maitama wanda tsohon Sanata ne daga 1999-2007 , a rasu a safiyar Juma’a a Kano yana da shekaru 76.
Abokin marigayin, Alhaji Hussaini Dalhatu ya shaida wa manema labarai cewa za a yi sallar jana’izar Sardaunan Dutse bayan sallar Juma’a a fadar Sarkin Kano.
Bello Maitama Yusuf, haifaffen garin Gwaram ne na jihar Jigawa, an haife shi a shekarar 1947, ya taba zama ministan harkokin cikin gida a shekarar 1981, ya kuma zama ministan kasuwanci a shekarar 1982.
Muna addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kyauta namu zuwan.
A wani labarin na daban a ranar Larabawa ne kungiyar kasashen Larabawa ta yi taro a birnin Alkahira na kasar Masar kan yadda za su kawo karshen mamayar da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa, da kuma hare-haren da take kaddamarwa a zirin Gaza.
Sanarwar da kungiyar ta fitar, ta ce an shirya taron ne, bayan neman agajin kasashen yankin da Falasdinu ta gabatar mata.
Wanda Ya Shuka Zamba, Shi Zai Yi Girbinta
Rikicin Sudan: Gwamna Lawal Ya Samar Da Agajin Ggaggawa Ga Daliban Zamfara 66
Harin da Hamas ta kaddamar a kan Isra’ila a ranar Asabar ta ce martani kan yadda sojoji ke ci zarafin Falasdinawa a masallacin Al-Aqsa, abin da ya sanya ta harbawa makwabciyar ta makaman roka da kuma cafke daruruwan Isra’ilawa.
Tsohon jagoran kungiyar Hamas, Khaled Meshaal ya bukaci kasashen musulmi da su fito zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu, inda ya bukaci kasashen makwabta da su taimaka musu wajen yakar kasar Isra’ila, yayin da ta ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan Falasdinawa.
Meshal wanda ke zaune kasar Qatar yanzu haka, ya ce gwamnatocin kasashen Jordan, Syria, Lebanon, da na Masar na ba da gudunmawar da ta kamata su bai wa al’ummar Falasdinu.
Da safiyar ranar Laraba ne, Isra’ilan ta kai hari garuruwan da ke kudancin Lebanon a matsayin martanin harin da Hesbollah ta kai mata a kan iyaka.
Source LEADERSHIPHAUSA