Rochas Okorocha ya halarci jana’izar surukar tsohon hadiminsa, Jemaimah Nwosu a Eziama Obierie Sanatan yace Gwamnoni shida sun kira shi su na son zuwa jana’izar, amma rashin tsaro ya hana.
Tsohon Gwamnan ya ba matasa shawarar su daina tada fitina, su yi amfani da katin zabensu a 2023.
Jaridar Punch tace tsohon gwamnan Imo kuma Sanata mai wakiltar yammacin jihar a yanzu, Rochas Okorocha, ya yi kira na musamman ga matasa.
Sanata Rochas Okorocha ya roki matasa su daina huce takaicinsu a kan sarakunan gargajiya, domin nuna rashin jin dadin yadda al’amura suke tafiya a Imo. Rochas Okorocha ya yi wannan jawabi ne a ranar Laraba, 22 ga watan Disamba, 2021, wajen jana’izar Jemaimah Nwosu a garin Eziama Obierie, jihar Imo.
Marigayiya Jemaimah Nwosu ita ce surukar Uche Nwosu, daya daga cikin abokan tafiyar Okorocha a siyasa, wanda ya nemi takarar gwamna a zaben 2019.
Bayan an birne wannan tsohuwa a Eziama Obierie, karamar hukumar Nkwerre, Sanata Okorocha ya yi jawabi, ya na mai kokawa a kan matsalar rashin tsaro.
Emeke Ihedioha ya hadu da Okorocha A cewar Rochas Okorocha, ana zubar da jinanen Bayin Allah babu gaira babu dalili a yau.
Vanguard tace magajinsa, Emeke Ihedioha ya halarci jana’izar. A maimakon matasa su rika yin ta’adi a al’umma, Okorocha ya ba su shawarar su jira zaben 2023, sai suyi waje da bara-gurbin shugabannin da ke kan mulki. Okorocha ya yi kuka yana cikin jawabi
An rahoto cewa tsohon gwamnan ya yi kuka, ya zubar da hawaye, ya na cewa ba a haka ya mika mulkin jihar Imo bayan ya kammala wa’adinsa a 2019 ba.
“Ba wannan ce Imo da nayi shekara takwas ina mulki ba. Ba na goyon bayan tarzoma, ina kira ku jira 2023, ku yi amfani da katin PVC, ku zabi nagari.” – Okorocha.
Da yake jawabi, Rochas Okorocha ya bayyana cewa gwamnoni shida sun gagara zuwa wajen jana’izar Nwosu saboda halin tsaro da kasar take fama da shi.
Garkuwa a mutane a Najeriya Kwanakin baya aka ji masu satar mutane sun yi gaba da wasu malaman addinin musulunci biyu a kauyen jihar Ogun; Ustaz Hussein AbdulJelil da Ilyas Jamiu.
Wadannan Bayin Allah sun kubuta, inda ‘Yan bindigan suka hakura suka karbi N2.2m bayan a baya sun hakikance a kan sai an biya fansar Naira miliyan 15.