Kungiyar goyon bayan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, TSO, ta ce tsoron Tinubu da Kashim Shettima ne yasa yan adawa suka fara babatu kan batun takarar musulmi da musulmi.
Mallam Abdulazeez Yinka Oniyagi, jagoran kungiyar ta TSO ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya yi a Jihar Kwara yana mai cewa za su shirya tattaki na mutum miliyan daya domin Tinubu.
Hon Aminu Suleiman, Direktan Kungiyar TSO na kasa ya ce da farko babu wanda ya yi batun tikitin musulmi da musulmi lokacin da Tinubu ya zabi Masari matsayin mataimaki har sai da ya zabi Shettima don suna tsoronsa shima.
Mallam Abdulazeez Yinka Oniyagi, Jagoran Kungiyar Goyon Bayan Tinubu (TSO) ya ce tsoron Tinubu da Shettima ne yasa masu adawa ke daukan nauyin masu dumama siyasa kan batun tikitin musulmi da musulmi.
Hakan ne zuwa ne a lokacin da Direkta Janar na TSO, Hon Aminu Suleiman ya ce kungiyar za ta koma ta yi nazari don kaucewa ‘kuskuren’ da jam’iyyar ta yi a Jihar Osun ranar Asabar.
Ya kara nuna gamsuwa cewa Asiwaju Bola Tinubu shine zai yi nasara a zaben 2023 duk da kayen da APC ta sha a Osun.
Dukkansu sun yi magana na a Jihar Kwara, yayin da suke bada alamun cewa za su shirya tattaki na mutane miliyan 1 domin dan takarar na APC.
Za mu koma teburin nazari don kada mu maimaita kuskuren da ya faru a Osun, Suleiman Gwamna Adegboyega Oyetola na APC ya sha kaye a hannun dan takarar PDP Ademola Adeleke inda ya samu kuri’u 403,371 gwamnan mai ci kuma ya samu 375,027.
A cewar Suleiman, “Za mu koma allon zane mu ga gyare-gyaren da za mu yi don tabbatar da cewa ba mu maimaita kuskuren da ya faru ba.”
A bangarensa, Oniyangi ya ce Tinubu ya shiga takarar da ayyukan da ya yi lokacin yana gwamnan Jihar Legas kuma labarin bata canja ba.
“Lokacin da ya nada Masari a matsayin mataimaki, babu wanda ya ce komai amma da ya karo Shettima wanda barazana ne ga yan adawa, labarin ya canja,” ya kara da cewa.
Source:legithausang