Ana Tsaka da Fargaba Kan Tsaro, Sojojin Kasa Sun Bayar da Lambobin Kiran Gaggawa.
A wani labari na daban, rundunar sojin kasan Najeriya, ta bada lambobi na musamman ga ‘yan kasa domin rahoto tare da kai bayanai kan duk wata barazanar tsaro.
Rundunar sojin kasan ta Najeriya ta wallafa lambobin ne a shafinta na soshiyal midiya a ranar Juma’a.
A cikin makonni biyu da suka gabata, tsoro da damuwa sun cika zukatan jama’a bayan wasu kasashen ketare sun bada shawarwari kan barazanar tsaro,kai farmakin ‘yan ta’adda a wasu sassan kasar nan.
Source:legithausang