Rundunar ‘yan sandan Kano da ke Nijeriya ta ce an jigbe karin sojoji da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro a fadin jihar don wanzar da tsaro gabanin hukuncin da Kotun Daukaka Kara za ta yanke a shari’ar gwamnan jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Mohammed Usaini Gumel ne ya bayyana haka a taron manema labarai da ya gabatar ranar Alhamis da maraice a birnin na Kano.
“Matsayar rundunar ‘yan sandan Kano da sojoji da sauran jami’an tsaro jihar ita ce, mun kammala hada gwiwa don daukar dukkan matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya kafin hukuncin Kotun Daukaka Kara da lokacinsa da kuma bayansa.
“Za ku ga cewa mun kara jami’an tsaro na dukkan hukumomin tsaro a muhimman sassa domin tabbatar da ganin ba a fuskanci karya doka da oda ba a dukkan sassan jihar nan,” in ji Kwamishina Gumel.
Wakilan APC da NNPP sun sanya a kan yarjejeniyar zaman lafiya a ofishin kwamishinan ‘yan sanda, in ji Kwamishina Gumel./Hoto: Rundunar ‘yan sandan Kano
Ya kara da cewa hukumomin tsaro sun tattauna da wakilan jam’iyyar APC da NNPP “kuma mun amince cewa hanya mafi a’ala ita ce ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin hukuncin Kotun Daukaka Kara da lokacin yanke shi da kuma bayansa.”
Kwamishinan ‘yan sanda Gumel ya ce,” Mun samu tabbaci daga jam’iyyun biyu cewa za su isar da sako ga magoya bayansu. Muna masu tabbatar muku cewa shugabannin jam’iyyun sun sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya a ofishin kwamishinan ‘yan sanda.”
Dangane da haka, rundunar ƴan sandan ta ba da shawarwari kamar haka:
i. Ba za a yarda da taron mutane a ko ina ba da kuma kowace irin manufa
ii. A guji shiga cikin manyan ayyuka da bayar da shawarar shirya zanga-zangar tashin hankali da yin zanga-zanga ko wasu tarukan murna da ka iya jawo martani daga wani ɓangaren.
iii. Ƴan siyasa su guji yin kalamai barkatai waɗanda ka iya haifar da tashin ko kuma ɓata shirye-shiryen samar da tsaro da taɓa fannin shari’a.
Source: TRTHausa