Fitaccen lauyan Najeriya kuma mai rajin kare hakkin bil’adama (SAN), Femi Falana, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da masu neman ballewa da sauran masu tayar da zaune tsaye a duk fadin kasar, kamar yadda tsarin mulikin kasa ya tanada.
Falana wanda ya bayyana haka yayin jawabi wajen taron kan cin hanci da rashawa, da aka shirya saboda ranar Demokradiya, Ya nuna adawa da umarnin gwamnatin tarayya na fito-na-fito da bata garen ko bude musu wuta, musamman a yankin Kudu Maso Gabas.
Yana mai cewa gwamnati ba ta da ikon shelanta yaki a kowane bangare na kasar ba tare da bin hanyar Majalisar Dokoki ta Kasa ba kamar yadda sashi na 304 na kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.
Shirin, wanda aka shirya tunawa da ranar dimokradiyya ta kasar, ya samu tallafi daga Gidauniyar MacArthur da Open Society Initiative for West Africa (OSIWA), da sauransu.
Babban lauyan ya ce duk da cewa babu wani dan Najeriya da zai goyi bayan tawayen yankin Kudu maso Gabas, amma ba daidai ba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ayyana yaki a kan mutanen yankin.
Shugaba muhammadu buhari yayi suna ta bangaren tare kudurorin tsarin mulki gami da amfani da karfi da ko in kula a kan wadanda ya ke gani matsayin barazana a sabgogin mulkin sa.
Baya bayan nan an shaidi take dokar kundin tsarin mulki a shari’ar shugaban darikar shi’a na kasar Mallam Ibraheem Zaksaky inda babbar kotun tarayya ta yanke hukuncin sakin sa tare da biyan sa tara bisa wahalar dashi da akayi shi da mai dakin sa tare da basu da laifin komi amma gwamnatin shugaba buhari ta kekasa kasa taki bin umarnin kotun ta gwamnatin tarayya.