Bayanai sun tabbatar da rasuwar shugaban kungiyar maharba ta Arewa Maso Gabashin Nijeriya, Muhammad Usman Tola, ranar Talata a Yola.
Wani jigon kungiyar kuma mataimakin mai bada shawara na musamman kan tsaro Yawalem, ya shaida wa LEADERSHIP HAUSA ta waya, cewa marigayin ya rasu ne a asibiti, bayan fama da ciwon ciki.
Ya kara da cewa “shugabanmu mutumin kirki, ya rasu yana da shekaru 72, ya bar mata hudu da yaya 13 da jikoki takwas.
“Muna rokon gwamnatin tarayya da ta Adamawa da kada a dauko wani da wani a dora mana a matsayin shugaba, ya kamata a bar mu mu zabi wanda ya dace da mu, domin kada a samu matsala a aikinmu na tsaro” in ji Yawalem.
Tarihi dai ba zai mance da muhimmiyar gudumuwar da marigayi Tola da kungiyar maharba suka bayar a yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram da masu aikata miyagun ayyuka a jihohin Arewa Maso Gabas ba.
A wani labarin kuma a cikin wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labaran ministan, Suleiman Haruna ya fitar, ya ce ministan ya bayyana hakan ne a wurin kaddamar da rabon kayan abinci ga mabukata a daukacin kasar nan.
Kaddamar da rabon dai ya gudana ne saura kwanaki uku ga bikin karamar sallah, a wani yunkuri na gwamnatin tarayya na rage hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar nan baki daya.
Ministan ya ce Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya damu matuka da yadda kayayyakin abinci suka yi tashin gwauron zabi a Nijeriya, wanda hakan ta sa ya amince da bayar da umurnin raba tan 42,000 na hatsi, wadanda suka hada da gero, dawa, masara da kuma shinkafa tan 60,000.
Ya ce shirin gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa za ta sake fasalin manufofinta na rage radadin kuncin rayuwa, wanda ba da jumawa za a shawo kan lamarin.
“Gwamnati tana kara kira ga ‘yan Nijeriya su kara ci gaba da hakuri da wannan kuncin rayuwa, mun dauki matakai da za su fitar da ku daga wannan mummunan yanayi. Ba zai gaza jaddada muku cewa wannan yanayin ba zai taba tabbata ba za mu kawo karshensa.”
Ya ce a yanzu haka an samu ragin shigowa da man fetur da kashi 50 duk wata, sannan an samu karuwar darajar naira wanda duk suna cikin shirin sake bunkasa ayyukan ci gaban al’ummar Nijeriya.
“A ‘yan kwanakin da suka gabata, gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shiri a bangaren wutar lantarki da nufin bunkasa fannin domin ‘yan Nijeriya su sami ishasshen lantarki.
“Abu mai muhimmanci ga wannan tsarin dai shi ne, Gwamnatin Tinubu ta bayar da kashi 85 na tallafin lantarki ga ‘yan Nijeriya wanda yakan ya tabbatar da kasancewarta gwamnatin dimokuradiyya mai goyon bayan al’umma tare da kara kahi 15 kacal na kudaden wutar lantarkin ga masu yawan samun wutan.
DUBA NAN: Hukumar Kashe Gobara A Kano Ta Ceto Dukiyar Miliyan 130
“Ina kira gare ku da ku ci gaba da goyon bayan Gwamnatin Tinubu a daidai lokacin da take aiwatar da tsare-tsareta domin sake fasalin tattalin arzikin kasa,” in ji shi.