Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta ceto sauran mata daliban jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara da ‘yan ta’adda suka yi garkuwa da su a ranar Juma’a.
Da ya ke Allawadai da garkuwa da daliban, shugaban kasa acikin wata sanarwa da kakakinsa, Ajuri Ngelale, ya fitar, ya ce, babu wani dalilin da zai sanya masu garkuwan su sace wadanda ba su ji ba su gani ba, kawai laifinsu shi ne don suna neman ilimi mai inganci, ya ce, wannan lamarin ba abun lamunta ba ne sam.
Yayin da shugaban kasan ya jajanta wa iyalan wadanda wannan lamarin ya shafa, ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na yin aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyar kowani dan Nijeriya.
A kan wannan aniyar, Tinubu ya bai wa iyalan wadanda aka yi garkuwa da su tabbacin cewa, gwamnati za ta yi dukkanin abunda ya da ce domin ganin daliban sun dawo cikin koshin lafiya.
Bugu da kari, shugaban ya sha alwashin cewa, gwamnatin tarayya za ta tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi sun cigaba da kasancewa wuraren samar da ilimi, sannan kuma an karesu daga aikace-aikacen ‘yan ta’adda.
A wani labarin na daban a kalla mutum 34 ne aka bada labarin cewa sun rasa rayukansu yayin da aka samu tashin wutar gobara a wani wajen ma’ajiyar Mai a Jamhuriyyar Benin yayin da wasu mutum 20 kuma suka samu munanan raunuka.
An ce, wutar ta tashi ne a wata haramtacciyar ma’ajiyar mai da ke Semi-Podji – wani garin da ke kan iyaka da Nijeriya.
Ministan kula da harkokin cikin gida na Jamhuriyar Benin, Alassane Seidou, ya shaida wa ‘yan jarida cewa, jarirai biyu na daga cikin wadanda suka mutu.
“Abun bakin ciki mutum 34 ciki har da jarirai biyu sun mutu. Gangar jikinsu ya kone sakamakon tashin wutar gobarar mai,” Seidou ya shaida.
Ya kara da cewa, a halin da ake ciki wadanda suka jikkata kuma suna kan amsar kulawar likitoci a asibiti.
Duk da cewar ministan bai bada wani karin haske kan masu safaran mai din ba, ana dai yawan samun safaran mai daga Nijeriya zuwa jamhuriyyar Benin.
Source: LEADERSHIPHAUSA