Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da babban jami’in Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPC) Mallam Mele Kyari, da gwamnan babban bankin Nijeriya, Godwin Emefiele a fadar gwamnati da yammacin yau Talata.
Ana kyautata zaton makasudin taron na da nasaba da kalaman Tinubu kan batun cire tallafin man fetur, wanda ya ambata a jawabinsa na rantsuwa a ranar Litinin.
Sakamakon tattaunawa kan batun cire tallafin man fetur, an fara samun layuka a gidajen mai.
Lamarin dai ya haifar da kunci da takaici a tsakanin al’ummar kasar nan.
Tattaunawar da Tinubu, Kyari, da Emefiele suka yi na kokarin ganin an magance matsalolin da kuma samar da mafita mai dorewa kan batun tallafin man fetur da ake ci gaba da yi.
A wani labarin daga kasar Sin kafin ranar yara ta duniya wato ranar 1 ga watan Yuni ta shekarar 2013, babban sakataren kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta Sin Xi Jinping ya taya yara murnar ranar a matsayin babban abokinsu. A cikin shekaru 10 da suka gabata, akwai abubuwa da dama da ba za a manta da su ba, da suka wakana tsakanin shugaba Xi da yara.
Yayin da shugaba Xi ya zauna da dalibai da malamai, ya kan kula da ko yara suna karatu da kyau, kana ya kan gayawa yara irin wasannin da yake so, da sa kaimi ga yara da su kiyaye lafiyarsu tare da motsa jiki. Ya jaddada cewa, lafiya ita ce tushen rayuwar dan Adam, don haka ya kamata yara su mai da hankali ga motsa jiki, kana iyalai da makarantu da al’umma, su samar da damar motsa jikin ga yara, don sa kaimi gare su wajen yin girma kamar itace.
Idan yara suna da buri, to al’ummar kasa tana da kyakkyawar makoma. Buri shi ne muhimmiyyar kalmar da shugaba Xi ya kan fada yayin da yake hira da yara. A duk lokacin da shugaba Xi ya zauna tare da yara, ya kan gaya musu su yi kokarin cimma burinsu da kaunar kasa tun daga kuruciyarsu.
Idan yara suna da karfi, to dukkan kasa za ta samu karfi. Shugaba Xi Jinping yana fatan yara za su samu karfi a sabon zamani, ta yadda al’ummar kasar Sin za ta samu kyakkyawar makoma a nan gaba. (Zainab)