Tinubu na son ƙarfafa dangantakar Najeriya da Afrika ta kudu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tattauna da takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, inda ya yi maraba da masana’antun hakar ma’adinai na kasar da su zuba jari a fannin bunkasa ma’adanai na Najeriya.
An gudanar da tattaunawar ce a ranar Litinin a birnin New York, gabanin babban taron Majalisar Dinkin Duniya.
A cewar wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya ci gaba da yunkurinsa na bunkasa tattalin arziki na diflomasiyya don jawo hankalin masu zuba jari a yayin ganawar.
“Kamfanonin hakar ma’adinai na Afirka ta Kudu suna da rawar da za su taka a fannin bunkasa ma’adanai a Najeriya,” in ji shugaban Najeriyar.
“Yan kasuwar ku sun kyautata sosai a harkar sadarwa ta Najeriya.”
“Muna da arzikin ma’adinai mai yawa a fadin kasarmu, kuma kuna da kwarewa sosai a wannan fannin.”
“Saboda haka, muna sa ran samar da ayyukan yi da kuma sakamako mai amfani a wannan fanni a matsayinmu na ‘yan’uwan juna.”
Tinubu ya kuma bukaci Afirka ta Kudu da ta haɗa kai da Najeriya wajen yin kira ga yin garambawul ga cibiyoyin hada-hadar kudi na duniya domin taimaka wa Afirka wajen yaƙar talauci da tabarbarewar tattalin arziki.